Thursday, February 5
Shadow

Kalli Bidiyon: Wallahi Ko America tazo ba zata iya magance matsalar Tsaron Najeriya ba>>Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, ko kasar Amurka ta zo Najeriya ba zata iya magance matsalar tsaron Najeriya ba.

Malam ya bayyana cewa da kasar Rasha ko China ne suka ce zasu kawowa Najeriya dauki za’a yadda dasu saboda a baya basu yiwa kasashe katsalandan a harkokin su na cikin gida.

Yace amma America ba da gaske take ba.

Yace kuma tunda sojojin Najeriya suka kasa magance matsalar, suma sojojin Amurka ko sun zo ba zasu iya magance matsalar ba.

Karanta Wannan  Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa zai tsaya takarar neman kujerar Sanata Natasha Hadiza Akpoti

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *