
Wasu ‘yan Arewa da aka tare a jihar Oyo yayin da suka je wucewa ta cikin jihar sun auna arziki inda duka suka tsere.
A baya irin wannan ta taba faruwa a jihar Edo inda aka dake wasu mafarauta wanda aka zarga da cewa masu garkuwa da mutanene har sai da suka daina motsi sannan aka cinna musu wuta.
Saidai a wannan Karin basu tsaya ba.
An ji mutanen dake magana a cikin Bidiyon suna kiran mutanen da ‘yan Bòkò Hàràm duk da yake cewa babu wata hujja data tabbatar da hakan.