
Bidiyon dan majalisa daga jihar Kano, Alhassan Ado Doguwa ya dauki hankula bayan da ya rika fadar Najeriya wasu na ce masa sai Atiku wasu na ce masa sai Tinubu.
Da ya dan yi muzurai, da ya kara cewa Najeriya aka ce masa sai baba.
A karshe dai yace baya son a rika raba masa hankali, shi bai san wani Baba ba Tinubu ya sani.