
Shahararren Mawaki, Idris Abdulkarim ya kalli idon da shugaban kasa, Seyi Tinubu ya gaya masa cewa, Mahaifinsa ce shugaban kasa, Mafi Muni da aka taba yi a tarihin Najeriya.
Idris ya fadi hakane a wajan wani taro da aka bashi dandamali yayi magana.
Bayan fadin maganar, an ga dan shugaban kasar ya tashi tsaye ransa a bace sai muzurai yake.
Da yawa dai sun jinjinawa Idris Abdulkarim bisa wannan mazantaka daya nuna.
Saidai dama can an sanshi da haka, a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, Idris Abdulkarim yayi wakar Najeriya Jaga-Jaga a wani dakin taro dake cike da manyan ‘yan siyasa.
Wakarce har yanzu idan dai za’a yi wani taro ko zanga-zanga ta nuna rashin jin dadin Gwamnati, to ita ake amfani da ita.