Wani dan kasuwa, Dr. Ugonna Osinachi Cliff Orabuchi, (Ikenga Ogberuru) daga jihar Imo ya saiwa surukinsa akwatin gawa na Naira Miliyan 130.
Rahotanni sun bayyana cewa, mutumin na da kyakkyawar ma’amala da surukin nasa tun yana da rai inda har gida ya sai masa dama wasu dake kusa dashi.
Lamarin dai ya dauki hankula da baiwa mutane mamaki musamman ganin yawan kudin da mutumin ya kashe.