Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa an jawo hankalinsa game da kananan yaran da gwamnatin tarayya ta gurfanar a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu ta hanyar zanga-zanga.
Gwamnan a sanarwar da ya fitar ta kafar X, ya bayyana cewa, ya baiwa kwakishinan Shari’a umarnin gaggauta yin abinda ya dace kan lamarin.
Ya karkare da cewa insha Allahu zai dawo dasu gida Kano.