Thursday, June 5
Shadow

Kalli Hotuna da Bidiyo yanda Ake zargin dan shugaban kasa, Seyi Tinubu yawa shugaban daliban Najeriya Tsirara yasa aka masa dukan kawo wuka jikinsa Duk burdi, kawai dan yace ba zai karbi Naira Miliyan 100 ba ya goyi bayan Tinubu

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Shugaban daliban Najeriya, Ya zargi dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da shugaban NTA da wasu hadiman shugaban kasar da gayyatarsa zuwa Legas dan ya karbi Naira Miliyan 100 ya ce yana goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Saidai yace ya ki amincewa da wannan bukata.

A wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta, An ga shugaban daliban yana cewa saboda ya ki amincewa da bukatarsu, sun sa an lakata masa duka aka dauki bidiyonsa tsirara aka kuma ce masa ko kasheshi aka yi babu abinda zai faru, za’a sa shugaban ‘yansanda ya binne maganar.

Yace sun tursasashi ya fito yace ya sauka daga mukamin shugaban daliban amma daga baya ya fito ya ce an matsa masa ne.

Karanta Wannan  Gwamnati ta sake kara farashin man fetur zuwa Naira 1070 akan kowace lita

Ya kara da cewa har yanzu bidiyonsa tsirara na cikin wayar dan shugaban kasar da wasu hadiman shugaban kasar inda yace be san abinda zasu yi da Bidiyonsa tsirara ba.

Wannan zargi nasa yasa mutane da yawa a kafafen sada zumunta sun fito suna neman a masa adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *