
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kai ziyara kudancin Najeriya inda aka ganshi a Coci.

El-Rufai da kansa ne ya wallafa wadannan hotunan inda yace ya halarci jana’izar wani me suna Chief Mathias Chidi Anohu ne a cocin.

Saidai da yawa sun ce Abin mamaki ne ganin El-Rufai a kudancin Najeriya musamman ma a coci.
Yaya kuna ganin akwai haske kuwa?