Thursday, January 16
Shadow

Kalli Hotuna: Jami’in Tsaron Gidan yari ya kashe abokin aikinsa saboda abinci a jihar Bauchi

Marigayi Aliyu Abubakar Ciroma.

Jami’in tsaron gidan yari a garin Burra dake karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi ya kashe abokin aikinsa sabosa Abinci.

Lamarin ya farune tsakanin Aliyu Abubakar Chiroma da Abokin aikinsa, Kabiru Abubakar wadanda suka jami’an tsrone na gidan yari koma kowa ya sansu Abokan junane.

Ranar da abin zai faru sun je cin abinci tare sai Chiroma ya ciro abincin nasa inda Kabiru yace zai ci, anan rigima ta kaure tsakaninsu inda Chiroma yace ba zai ci mai abinci ba.

A hakane sai Kabiru yawa Ciroma karo da kai, inda nan take ya fadi baya motsi.

An garzaya dashi babban Asibitin Burra inda likitoci suka tabbatar ya mutu.

Karanta Wannan  Mata a yi hattara, Wannan sabulun na kona fata

Tuni aka kama Kabiru. Shugaban karamar hukumar Ningi, Hon Nasiru Zakari ya tabbatar da faruwar lamarin inda shima kakakin hukumar gidan yari ta jihar Bauchin, Ahmad Usman Tata ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *