Sunday, May 25
Shadow

Kalli Hotunan Gawurtaccen me Gàrkùwà da mutane da jami’an tsaro suka kama

Jami’an tsaro sun kama masu garkuwa da mutane dan karbar kudin Fansa su biyu a Barkin Ladi dake Jihar Plateau.

Rahoton yace an kama su ne bayan da wasu da aka kama a baya suka bayar da bayanai akan maboyarsu. Kuma an kamasu ne a kauyen Lugere Sho.

Hakanan an kara kama wani me garkuwa da mutanen a Kauyen Kwok duk dai a Barkin Ladi kuma yana bayar da bayanai game da ta’asar da yayi a baya ciki hadda garkuwa da mutane a jiharta Filato da Nasarawa.

Hakanan ya bayar da bayanai akan wadanda suke aiki tare da maboyarsu inda jami’an tsaro tuni suka bazama dan nemosu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Attalili ya bayyana sunayen Annabawa da ba'a taba jinsu ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *