
A jiyane dai muka samu Rahoton cewa, Giwaye sun bayyana garin Kala Balge na jihar Borno inda mutane suka taru suna kallonsu.
Zagazola Makama yace giwayen sun rika cinye amfanin gona inda yayi kira ga mahukunta dasu kaiwa jama’a dauki.
Bidiyon da hotunan giwayen sun ci gaba da yaduwa a kafafen sada zumunta
Wasu rahotanni sun ce giwayen sun shiga garin ne daga kasar Chadi.