Saturday, May 31
Shadow

Kamata yayi ka yi hakuri ka barwa dan kudu ya tsaya takara a 2027>>Wasu ‘yan PDP daga kudu suka gayawa Atiku

Atiku Abubakar 2011 President campaign Photo by www.mortenfauerby.dk ©mortenfauerby 2010 – all rights reserved

Wasu ‘yan PDP daga Kudancin Najeriya sun baiwa Atiku Abubakar bakin cewa ya hakura da maganar tsayawa takara a shekarar 2027 ya barwa dan kudu.

Sun ce ba ma Atiku kadai ba, duk wani dan Arewa kamata yayi ace ya hakura da tsayawa takara a barwa dan kudu ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

Kungiyar tace dama can Atiku ne ya fara jawowa jam’iyyar PDP koma baya a shekarar 2014 inda ya jagoranci gwamnoni 5 suka fice daga jam’iyyar suka koma APC suka juyawa Goodluck Jonathan baya.

Shugaban kungiyar, Dennis Shima ne ya fadi haka inda yace ya kamata a bar dan kudu ya kammala shekara 8 kamar yanda Buhari yayi

Karanta Wannan  Tonon Silili, Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya haura shekaru 90 ba 88 kamar yanda yake ikirari>>Inji Tsohon Gwamnan Ogun, Amosun

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *