Friday, December 5
Shadow

Kamfanin DSTV da sauran tashoshi na Tauraron dan Adam sun tafka asarar Dala Miliyan $158.19 saboda ‘yan Najeriya da yawa yanzu sun daina saka kati saboda matsin tattalin arziki

Rahotanni sun ce Kamfanin Multichoice wanda su DSTV suke karkashin sa sun tafka mummunar asara saboda ‘yan Najeriya da yawa sun daina saka kati suna kallon tashoshin.

Kudin shigar kamfanin a shekarar data gabata yayi kasa da kaso 44 cikin 100 inda a yanzu suka samu kudin shiga da ya kai dala Miliyan $197.74.

Saidai a shekarun baya suna samun kudin shiga da ya kai dala Miliyan $355.93.

Hakan na nufin sun tafka asarar dala Miliyan $158.19 idan aka kwatanta da shekarar data gabata.

Lamarin dai bai zowa mutane da mamaki ba musamman ganin yanda kasar ke cikin hali na matsin tattalin arziki.

Karanta Wannan  WATA SABUWA: Idâɲ Kara Fitòwa Ka Çì Mùtùñcìñ Malamai, Saì Muñ Toñà Maka Asìri, Sakon Shêikh Albanin Gombe Ga Dan Beĺlo

Hakan kuma baya rasa nasaba da karin kudin subscription da DSTV din suka yi daga Naira N29,500 zuwa Naira 37,000 duk wata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *