Wednesday, January 15
Shadow

Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya dakatar da shigo da man fetur daga kasar waje inda ya amince ya saya daga wajan Dangote

Kamfanin Man fetur na kasa,NNPCL ya dakatar da sayo man fetur daga kasar waje inda ya amince ya sayi man fetur din daga wajan Matatar man fetur din Dangote da sauran matatun man fetur masu zaman kansu.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ya bayyana haka a wajan wani taro da ya faru a Legas ranar Litinin.

Hakan na zuwane yayin da ‘yan kasuwar man fetur suka nace saidai su sayo man fetur din daga kasar waje maimakon sayowa daga hannun matatar man Dangote saboda a cewarsu,man fetur din da suke kawowa daga wajen ya fi na Dangote sauki.

Kyari ya kuma musanta cewa suna yiwa matatar man fetur ta Dangote zagon kasa inda yace suma suna da hannun jari a matatar.

Karanta Wannan  Lalacewar wutar Lantarki:Majalisa ta gayyaci ministoci dan binciken yanda aka yi da Dala Biliyan $2 da aka bayar da samar da wutar Lantarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *