
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur dinsa a Abuja da Legas zuwa Naira 875 da kuma Naira 900.
Hakan na zuwane kwanaki bayan da NNPCL din ya kara farashin zuwa Naira N915 da kuma Naira N955.
Saidai a ranar Laraba, kafar TheCable ta ruwaito cewa, ta lura kamfanin ya rage farashin zuwa Naira 40 akan kowacce lita.
A legas, Farashin ya ragu zuwa N875, sannan a Abuja farashin aguwa yayi zuwa N900.
Saidai rahoton yace Dangote da Mobil da AP duka basu rage farashinsu ba yana nan a Naira 915 kan kowace lita.