Monday, December 16
Shadow

Kanunfari yana maganin sanyi

Tabbas Kanunfari yana maganin sanyi kamar yanda masana ilimin kiwon lafiya suka tabbatar.

A mafi yawancin lokuta akan hada Kanunfari da zuma ne dan samun sakamakon maganin sanyi me kyau.

Masana sun bayyana hadin Kanunfari da zuma a matsayin na gaba-gaba wajan magance matsalar sanyi da mura.

A yayin da mutum ke fama da kaikayin makogoro, shima wannan hadi na da tasirin da zai magance wannan matsalar.

Yanda ake hadin shine:

Za’a samu Kanunfari kamar kwaya 6 a dan dorasu a wuta a dan gasa.

Sannan a daka su su zama gari.

Sai a zuba babban cokali na zuma a ciki.

Ana shan wannan hadi sau biyu zuwa uku a kullun dan maganin tari mura da kaikayin makogoro.

Karanta Wannan  Amfanin kanunfari da madara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *