Friday, December 5
Shadow

Karanta Cikakken bayani kan Rayuwar AM. Yerima, Shekararsa Nawa, Dan wace jihane, kuma waye mahaifinsa na gaskiya?

Tun bayan da aka samu wata hatsaniya a ranar Talata da yamma 11 ga watan nan na Nuwamba 2025, a tsakanin ministan babban birnin Najeriya, Abuja, Nyesom Wike da jami’an sojin ƙasar saboda sojojin sun hana ministan shiga wani fili, ake ta yaɗa labarai da ra’ayoyi daban-daban a kan lamarin.

Baya ga fassara da ake yi wa lamarin ta ɓangarori daban-daban – na siyasa da mulki da kuma dokoki da ƙa’idoji na mulki, wani abu kuma da ke ɗaukan hankalin jama’a shi ne, jagoran sojojin da suka yi wannan dambarwa da ministan na Abuja da tawagarsa.

Jagoran tawagar sojojin shi ne Laftanar AM Yerima, wanda matashin ƙaramin hafsan sojin ruwa na Najeriya ne, wanda kuma ya kasance ne a wajen bisa umarnin mai gidansa tsohon shugaban rundunar sojin ruwa ta Najeriya, Vice Admiral Awwal Zubairu Gambo (mai ritaya), wanda shi ne mai filin da ake taƙaddama a kansa.

Karanta Wannan  Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un: Kalli Bidiyon dan gidan tsohon Gwamnan Kaduna, Ibrahim El-Rufai na cewa shi bai yadda da Allah ba sannan ya tsànì Hausawa

Abin da ya faru a tsakanin ministan na Abuja da wannan matashin soja ya ɗauki hankalin jama’a da dama, musamman yadda wasu ke mamakin yadda wannan matashin sojan ya kasance a lokacin ba tare da nuna wata fargaba ko tsoro ba.

A dangane da wannan abu da wasu ke ganin kamar wata jarunta ce sojan ya nuna, duk da irin kalamai da barazana da Wike yake yi masa a lokacin, BBC ta yi nazari kan rayuwar wannan matashi, Laftanar AM Yerima.

Wane ne AM Yerima?

Sunansa Laftanar Ahmed Yerima kuma sojan ruwa ne wanda aka haifa a birnin Kaduna kuma ya girma a can da kuma birnin Fatakwal na jihar Rivers, duk da cewa ɗan asalin garin Fune ne da ke jihar Yobe.

Karanta Wannan  Kalli hotunan yanda ake ginin tashar jirgin kasa ta zamani a Kano

A shekarar 2011 ne Ahmed Yarima, mai shekaru 33 da haihuwa ya fara karatu a sashen koyar da aikin jarida a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Wani abokin karatun Yerima ya shaida wa BBC cewa suna yi wa matashin laƙabi da MD.

“Tun a lokacin matashi ne siriri, dogo kuma marar tsoro sannan kuma mutum ne mai iya hulɗa da abokan karatunsa.”

To sai dai kuma bayan Yerima ya bar jami’ar Ahmadu Bello bayan shekara ɗaya sakamakon samun gurbi a kwalejin horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna a 2012.

Yerima ya fito a matsayin Laftanar na sojan ruwa a shekarar 2017.

A 2018 ne Yerima ya fara atisayen haɗa na ƙasa da ƙasa domin yaƙar ta’addanci da ake kira da “Exercise Flintlock” a birnin Agadez da ke jamhuriyar Nijar

Karanta Wannan  Bidiyo Da Duminsa: Mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti sun fara zaben dan yi mata kiranye ta sauka daga wakilcinsu da take a majalisar Dattijai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *