
Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun musanta jita-jitar da ke cewa wasu daga cikinsu Guda biyar na Goyon bayan tikitin El-Rufai/Obi a zaɓen 2027.
Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Dakta Emmanuel Agbo, ya fitar a madadinsa a yau Asabar.
Ya ce, “Wajibi ne a gare mu a matsayin ƙungiyar Gwamnonin PDP, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, mu fito mu karyata, kuma mu yi Allah-wadai da wadannan jita-jita marasa tushe da wasu ‘yan siyasa masu son zuciya ke yayatawa. Su ne dai ba za su iya jure irin kokarin da muke yi don nuna gazawarsu a shugabanci ba, wanda ya jefa ‘yan Najeriya cikin fatara da tsananin wahala.”
“A saboda haka, ƙungiyar gwamnonin PDP ba ta da wata alaka da waɗannan mutane, kuma ba ta da wani shiri na goyon bayan wata yarjejeniya da wasu ke ƙoƙarin yi a bayan fage don marawa tikitin Nasir El-Rufai/Peter Obi baya a zaɓen 2027.”