Monday, December 16
Shadow

Kasar Amurka ta ki yadda ta bayar da bayanai akan rayuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda tace wakilintane dake taimaka mata wajan cimma burikanta

A yayin da aka shigar da wata kara a kotun kasar Amurka ake neman bayanai game da rayuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a baya inda ake zargin ya yi ta’ammuli da kwaya da kuma maganar ingancin takardun karatunsa, kasar Amurka tace ba zata bayar da wadannan bayanai ba.

Dan jarida, David Hundeyin ne ya shigar da kara yake neman bayanai akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kuma tun a shekarar data gabatane dai kotun kasar Amurka ta ki yadda ta bayar da bayanan da yake nema.

Dan jaridar yace hukumomin kasar Amurka, CIA, FBI, da DEA sun shigar da kara inda suma suke neman cewa kada a bashi bayanai akan shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu inda CIA wadda kungiyar leken Asiri ce ta kasar Amurka tace Bola Ahmad Tinubu wakilinta ne da take amfani dashi wajan cimma muradunta.

Karanta Wannan  Yanzu Haka Wasu Ministocin Shugaba Tinubu Ba Sa Iya Ganinsa, Don Su Gaya Masa Matsalar Da Kasa Ke Ciki, Balle Kuma ‘Yan Majalisar Dokokin Kasar Da Ba Su Da Damar Ganawa Da Shi Domin Su Tattauna Matsalar Al'umma, Inji Sanata Ndumi

Zuwa yanzu dai fadar shugaban kasa bata mayar da martani game da wannan zargin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *