Kasar Faransa ta bayyana cewa ta daina sayarwa da kasar Israela makamai saboda kisan Falas-dinawa da kasar ta Israela ke yi.
Sanarwar hakan ta fito ne daga kasar ta Faransa bayan da yaki tsakanin Israela da Hamas ya dauki tsawon kusan shekara guda ana yi.
Israela dai ta kashe mata da yara da fararen hula da dama a yakin wanda da yawa ke bayyana cewa tanawa Falasdinawan kisan kare dangine.
Da yawa sun ji dadin wannan mataki da kasar ta Faransa ta dauka inda rahotanni suka ce Faransar kuma ta yi kira ga sauran kasashen dakw sayarwa Israela makamai su daina.
Ta kara da cewa tana son a dauki hanyar diflomasiyya a matsayin wadda zata kawo karshen wannan rikici.