Saturday, December 13
Shadow

Kasar Saudiyya ta dakatar da bayar da Bizar zuwa aiki ga ‘yan Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, Kasa Saudiyya ta dakatar da bayar da Bizar aiki ga ‘yan Najeriya da sauran kasashe masu yawa.

Kasashen da wannan lamari ya shafa sun hada da Indonesia, Iraq, Jordan, Yemen, India, Pakistan da Bangladesh.

Sauran sune Egypt, Algeria, Sudan, Ethiopia, Tunisia da Morocco.

Rahoton yace, Ma’aikatar kula da ci gaba al’umma da kasar Saudiyyar ne ta sanar da hakan.

Kuma an dauki wannan mataki ne dan baiwa mahajjata damar gudanar da aikin Hajji, idan aka kammala aikin Hajji nan da karshen watan Yuni za’a ci gaba da bayar da bizar.

Karanta Wannan  Yadda Tinubu Ya Gwangwaje 'Yan Super Falcons Da Kyautar Dala 100,000 Da Kuma Gida Kowannen Su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *