Tuesday, February 24
Shadow

Kasuwar Onitsha zata ci gaba da kasancewa a kulle har na tsawon sati daya>>Inji Gwamna Soludo

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya sake nanata cewa, Kasuwar Onitsha zata ci gaba da kasancewa a kulle har na tsawon sati daya.

Yace idan kuma litinin ta zo ‘yan kasuwar suka ki budewa, kamar yanda suka saba, zai sake kulleta na tsawon sati biyu.

Yace tunda hutu suke so, zai taimaka musu su huta da kyau.

Hakanan yace idan aka ci gaba da kulle kasuwar, zai kwace shagunan masu kulle shagonsu ya baiwa wadanda suka shirya yin kasuwanci.

Hakan na zuwane yayin da ‘yan kasuwar suka fito suka tare babbar gadar Onitsha suka hana shiga da fita daga garin.

Karanta Wannan  Bincike: Karanta Jadawalin jihohin da aka fi samun matan aure na aikata Zìnà, 'yan mata ma na lalata, Rahoton yace babu irin wadannan matan ko daya a jihohin Jigawa, Katsina da Kebbi sannan Kuma jihar Taraba ce ta daya a Arewa wajan aikata wannan masha'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *