
Kungiyar Kwadago NLC ta bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta gaggauta biya mata bukatunta nan da kwanaki 7 ko kuma ta tsunduma yajin aiki.
Kungiyar ta bukaci gyaran Fansho ne da kuma zargin karkatar da wasu kudaden ma’aikata.
Hakan na kunshene a cikin sanarwar da shugaban kungiyar Joe Ajaero ya sakawa hannu.
Yace idan gwamnati bata biya musu bukata ba nan da kwanaki 7 akwai yiyuwar su shiga yajin aiki