
Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarkashin jagorancin alƙali Emeka Nwite ta amince da bayar da belin tsohon ministan shari’a Abubakar Malami da iyalinsa kan kuɗi naira miliyan 500 da kuma mutum biyu da za su tsaya musu.
A cewar alƙalin, mutanen da za su tsaya musu sai sun kasance suna da filaye a yankunan Asokoro da Maitama ko Gwarinpa, sannan kuma sai sun miƙa dukkan takardun tafiyarsu ga kotu.
Kwanakin baya ne dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta gabatar da tuhume-tuhume 16 a kan Malami da iyalinsa masu alaƙala da halasta kuɗaɗen haram da kuma mallakar kadarori da darajarsu ta haura naira biliyan 8.7 wanda ya kai ga tsaresu a gidan yarin Kuje da ke Abuja.