
Babbar Kotun jihar Delta ta yi doka inda tace hana ‘yan kasa da shekaru 16 samun gurbin karatu a jami’o’in Najeriya da hukumar JAMB ke yi ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.
Karar wadda aka sakawa sunan John Aikpokpo-Martins v. Joint Admissions and Matriculation Board (JAMB) & four ohers ta kalubalanci JAMB kan hana ‘yan kasa da shekaru 16 shiga jami’a.
Mai shari’a, Hon. Justice Anthony O. Akpovi ya amince da bukatar masu kara inda yace hukumar JAMB ta sabawa ka’ida idan tace ‘yan kasa da shekaru 16 ba zasu samu gurbin karatu a jami’o’in Najeriya ba.
Da wannan hukunci, a yanzu kotun tace duka jami’o’i su rika daukar dalibai da suka cika sharudan dauka gurbin karatu ba tare da la’akari da shekarunsu ba.
A ranar 16 October 2024 ne JAMB ta fito da sabuwar dokar hana ‘yan kasa da shekaru 16 shiga jami’a.