Monday, March 23
Shadow

Kotu Ta daure Tsohon Akanta janar na Najeriya Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku tsawon shekaru 72 saboda satar Naira Miliyan N868.4

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta daure tsohon Akanta Janar na kasa, Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku bayan samunsa da laifin satar kudade da suka kai Naira Miliyan N868.4

Mai shari’a, Justice James Omotosho ne ya yanke masa hukuncin ranar Litinin bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar masa kan zargin.

An zargeshi da saka kudi a wasu asusun bankunan kamfanoni 4 wanda a baya ya karyata yace bai ma taba jin sunayen kamfanonin ba.

Saidai daga baya ya amsa cewa lallai ya tura kudade zuwa asusun ajiyar kudi na wadannan kamfanonin.

Kamfanonin sune kamar haka: Temeeo Synergy Concept Limited, Turge Global Investment Limited, Laptev Bridge, sai kuma Arafura Transnational Afro Limited.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Na yafewa Dr. Hussain Kano Zhaghin da ya min saboda tuban da yayi daga Dariqa ya komo Sunnah>>Inji Baffa Hotoro

Chukwunyere Anamekwe Nwabuoku a yanzu dai shekarunsa 64 a Duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *