Friday, December 12
Shadow

Kotun Ƙolin Najeriya ta soke Afuwar da shugaba Tinubu yawa Maryam Sanda

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Maryam Sanda bisa samunta da laifin kashe mijinta Bilyaminun Bello.

Alƙalan kotun guda huɗu a cikin biyar ne suka tabbatar hukuncin, inda ake yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan watsi da ɗaukaka ƙararta, kamar yadda mai shari’a Moore Adumein ne ya sanar da hukuncin a madadin sauran alƙalan.

Kotun ta ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi rangwame ga Maryam alhalin ana ci gaba da sauraron shari’arta a gaban kotun ɗaukaka ƙara, kamar yadda tashar Channles ta ruwaito.

A ranar 27 ga watan Janairun 2020 ne kotu a Abuja ta yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin da kashe mijinta Bilyaminu Bello a gidansu na Abuja shekarar 2017.

Karanta Wannan  Godswill Akpabio ya maka Sanata Natasha Akpoti kara a kotu inda yake neman ta Biyashi diyyar Naira Biliyan 200 saboda bata masa suna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *