Thursday, April 2
Shadow

Ku dawo jam’iyyar PRP tunda ADC ta rikice>>Inji Shugaban jam’iyyar PRP

Shugaban jam’iyyar PRP James Adeshina ya yi kira ga su Atiki Abubakar, da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Abubakar Malami da sauransu cewa, su bar jam’iyyar ADC su dawo PRP tunda jam’iyyar ta ADC ta rikice.

Ya bayyana hakane ga manema labarai inda yace abin takaici ne ganin yanda babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ADC ta shiga rikici.

Wani me suna Nafiu Bala da ya kai su Atikun kotu ya bayyana cewa, shine shugaban jam’iyyar ta ADC ba David Mark ba inda hakan yasa INEC ta cire sunan David Mark daga kundin tattara bayananta har sai an kammala shari’ar a kotu.

Karanta Wannan  Kalli Wata 'yar kasar Uamdana murna da samun Visar Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *