
Gwamnatin tarayya ta bakin Hukumar kula da yanda ake kasuwanci da baiwa ‘yan Najeriya kariya, (FCCPC) tace Kamfaninn Meta me Facebook da Instagram da WhatsApp ko da ya bar Najeriya sai ya biya tarar da aka kakaba masa.
An kakabawa kamfanin tarar Dala Miliyan $290 bisa zargin aikata ba daidai ba da bayanan ‘yan Najeriya dake amfani da manhajar.
Saidai kamfanin yayi barazanar barin Najeriya.
Wakilin Hukumar FCCPC, Ondaje Ijagwu, ya bayyana cewa an yiwa kamfanin na META irin wannan tarar a Texas ta kasar Amurka da kasashen Turai da India, South Korea, France da Australia amma duk bai yi barazanar barin wadancan kasashe ba sai Najeriya.
Yace kamfanin ya fadi waccan maganane kawai dan ya jawo hankalin mutane amma ya sani ko ya bar Najeriya sai ya biya tarar da ake binsa.