Ku Yi Amfani da Shafukan Sada Zumunta Wajen Ƙarfafawa Ƙasa, Ba Raba Kan Jama’a Ba, Sakon Shugaba Tinubu Ga Matasa.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga matasan Najeriya da ke da tasiri a kafofin sadarwar zamani da su yi amfani da wannan damar wajen haɗa kan al’umma da ƙarfafa cigaban ƙasa. Ya jaddada muhimmancin tantance gaskiyar bayanai kafin yada su, yana mai cewa karfin da kafafen ke da shi na da tasiri a fagen cigaba da haɗin kai haka kuma amfani da su ta mummunar hanya na iya haifar da rikici.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron Progressives Digital Media Summit da aka gudanar a Abuja, mai taken “Unveiling the Critical Role of New Media in National Development.” Ya ce matasa sun fara nuna kwarewa ta hanyar kirkire-kirkire da amfani da fasahar zamani don wayar da kai, samar da ayyuka, da kuma ba da gudummawa ga cigaban kasa.
A nasa jawabin, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya yaba da irin rawar da masu amfani da kafafen sadarwa ke takawa wajen kare muradun Najeriya a idon duniya.
Haka zalika, mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya ja hankalin mahalarta taron kan yadda ya kamata a fuskanci ƙalubalen da ke tattare da yaɗuwar labaran ƙarya, da sauran barazanar fasahar zamani.