
Rahotanni sun bayyana cewa, Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya Biwa mahaifinsa, Joshua Nlemanya Wike dan shekaru 90 fili a Abuja.
Rahoton yace Wike ya baiwa mahaifin nasa filinne a Guzape II wanda darajarsa ta kai ta Naira Miliyan 400.
Hakanan bayan mahaifinsa akwai ‘yan uwansa maza da mata da abokai da ya baiwa filayen a Abuja.
Hakan na zuwa ne kwanaki bayan da aka zargi Wike da baiwa ‘ya’yansa filaye a Abujan, zargin da ya karyata yace Atiku ne ke son bata masa suna.
Rahoton yace mutane 38 ne Wike ya baiwa ma’aikatansa yace a basu filaye, ma’aikatan da yawa sun yi mamakin wannan abu, kamar yanda peoplesgazette ta ruwaito.