
Wata Kungiyar magoya bayan Peter Obi wadda Alhaji Ahmad Abulfathi ya kafa tace sun rushe kungiyar tasu inda suka koma goyon bayan kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Kungiyar tace duka rassanta na kasa an rushe su inda suka koma goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Kungiyar tace ta yanke shawarar yin wannan hadaka ne sabida hadin kai sannan ta gano cewa duk da kalubalen da ake fuskanta a mulkin Tinubu amma ai sai an sha wuya akan sha dadi.