Saturday, June 27
Shadow

Kungiyar Magoya bayan Peter Obi sun koma goyon bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka ce shine zai kai Najeriya ga ci

Wata Kungiyar magoya bayan Peter Obi wadda Alhaji Ahmad Abulfathi ya kafa tace sun rushe kungiyar tasu inda suka koma goyon bayan kungiyar magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Kungiyar tace duka rassanta na kasa an rushe su inda suka koma goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Kungiyar tace ta yanke shawarar yin wannan hadaka ne sabida hadin kai sannan ta gano cewa duk da kalubalen da ake fuskanta a mulkin Tinubu amma ai sai an sha wuya akan sha dadi.

Karanta Wannan  Ji yanda aka kama wasu 'yan Najeriya na shirin shiga kasar Ingila da wani yaro da suka sata daga Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *