Kwamishinan Ma’aikatar Sanya Idanu a ayyukan gwamnati, Mohammed Diggol ya ajiye aiki.
Labarin hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa a Ranar Lahadi a wata sanarwa da ya fitar a Kano.
Tun da dare, Diggol shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Sufuri kafin daga bayan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya canja masa ma’aikata.
Sai dai kuma kwanaki kadan da bashi sabuwar ma’aikatar Sa’id Diggol ya sanar da ajiye aiki a matsayin Kwamishina a gwamnatin Abba.
Dawakin-Tofa ya ce Gwamna Abba ya karbi takardar ajiye muƙamin, inda ya kuma godewa Diggol tare da yi masa fatan alheri s rayuwarsa.