Thursday, June 5
Shadow

Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa

Kwamishina ya mayar da Naira miliyan 301 ragowar kuɗin ciyarwar azumi a Jigawa.

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Auwalu Danladi Sankara, ya mayarwa baitul malin jihar Naira miliyan 301 da su ka yi ragowa bayan kammala shirin ciyarwa na watan Ramadan bana.

Sankara ya sanar da mayar da kudaden ne a yayin taron majalisar zartarwa na jiha wanda gwamna Malam Umar Namadi ya jagoranta.

Kudin sun yi ragowa ne biyo bayan ware naira biliyan 4.8 da gwamnatin jihar Jigawa ta baiwa ma’aikatar don shirin ciyar da abinci, wanda ya kunshi dukkanin kananan hukumomi 27 da kuma cibiyoyi kusan 700 na ciyarwa.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa:Ji yanda na kusa da Buhari ke nuna basu tare da Tinubu

An ba da rahoton cewa, shirin wanda wani kwamiti ya jagoranta, ya ciyar da mutane sama da 5,550 a kullum a tsawon kwanaki 29 na azumi.

Majalisar zartaswar jihar ta yaba wa matakin da kwamishinan Sankara ya dauka na dawo da ragowar kuɗin, inda ta bayyana hakan a matsayin wani abin yabawa da nuna gaskiya da rikon amana da kuma tattalin dukiyar al’umma.

Daily Nigeria Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *