Sunday, May 3
Shadow

Kwankwaso yayi cikakken bayani kan barin jam’iyyar ADC da komawarsa NDC da kuma maganar fitowa takarar shugaban kasa

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa irin rikicin da yasa sua bar jam’iyyar NNPP yanzu haka ya mamaye jam’iyyar ADC.

Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta inda yace dan hakane suka fara neman jam’iyyar da zasu sake komawa dan ci gaba da fafutuka.

Yace a yanzu haka suna magana da jam’iyyar NDC da PRP.

Kwankwaso yace kuma maganar fitowa takarar shugaban kasa ko goyon bayan wani dan takarar shugaban kasa duk babu gaskiya a cikinsu.

Sannan yace da ba’a ganshi ba a wasu tarukan jam’iyyar ADC, wani uzuri ne ya hanashi kuma ya sanar da shugabancin jam’iyyar.

Karanta Wannan  Da Duminsa: EFCC sun tabbatar da cewa malam Nasiru Ahmad El-Rufai a wajansu zai kwana suna masa tambayoyi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *