Monday, December 16
Shadow

Labarin soyayya

LABARIN SOYAYYA ME BAN TAUSAYI

Wata yarinya ce tana yawan zuwa wani studio ta saye CD
cassete a wajen wani saurayi, ashe son shi ne take yi, duk
lokacin da taje sayen cassete sai ta tsaya suyi hira, har ta fada
masa gidan su, ta bashi labarin iyayen ta.
Watarana sai tayi kwana bakwai bataxo ba! Sai saurayin nan
yaje gidansu da tayi masa kwatanci, domin ya tambaya lafiya
kwana 2 bai gane ta ba, bayan yaje, ya aika yaro sai mahaifiyar
ta ta fito, ta fada masa ai yau sati daya da rasuwar yarinyar,
nan take ya fadi ya suma, bayan an watsa masa ruwa ya
farfado… Yayi zugum Yana kallon su, sai mahaifiyar tace ya
shigo cikin gidan, ya shiga, ta jashi ta kai shi har dakin yarinyar,
suna shiga yaga hoton sa manne a bango, mahaifiyar ta bashi
labarin irin yanda yarinyar ke son shi, ta dauko tulin kasusuwan
da yarinyar ke saye daga gareshi, tace ka gansu bata taba
bude ko daya ba, na sha gaya mata idan taje wurin ka, ta fada
ma tana son ka. Ta aje kasusuwan kusa gareshi, ya diba su
daya bayan daya, ba wanda aka bude.
Ashe tana zuwa ne ta saye cassete, don kawai ta gan shi suyi
hira, sai kawai ya fashe da kuka! Mahaifiyar tace lafiya? Sai ya
bude mata cassete guda taga wasika a ciki, ashe shima duk
cd da ta saye sai ya rubuta mata wasikar soyayyarshi aciki.
Yan uwa maxa da mata in kanason mutum ka fada masa, kar
kayi zurfin ciki.

Ga wani labarin:

Wata rana Wani Saurayi Yaje wurin wata Budurwa da niyar Fasikanci sai yaje ya Gaya mata sai taki Amince wa Sai ya tafi Sai Bayan ya qara Dawo wa sai Yace mata ta Amince Da Abunda yake buqata tace bazata Amince Ba yace mata ya Bata duka Dukiyarsa Tace Bata So Amma Tana So yayi Abu guda Idan Har yayi wallahi Zata Amince Sai yace mata Ta fadi Komi nene Zaiyi Tace Masa Tana so ya Tsaida Salla kar ya sake yayi wasa da ita Har Tsawon Kwana 40 to Idan Har yai Haka Wallahi Zata Amince yace To Shikenan Zai Kwatanta Sai ya tafi da yaji Anyi Kiran Salla kafin liman ya Shigo shi har ya Rigashi Shi Kullum Haka Yai Tayi Aka kai kwana 10 aka kai 20 aka kai 30 Ana cika Rana Ta 40 kawai sai Yarinyar nan tazo tace yau ne zata Cika Mashi Alqawarin Da Ta Dauka Sai Yace Subahanallai Allah ya Shiryeki to jamaa Cika Salla akan lokaci tana Hana Alfasha Kaman Yadda Allah yake Fada a cikin Suratul-Ankabut Aya ta (45) (“Innas-salata Tanha anil fahsha’i Wal-Munkar) zuwa Karshen Aya Allah yasa Mu Dace ya kuma tsare mu Daga Aikin shedan Al-barkar Annabi Muhammad (S.A.W.) ya Allah ka tsaremu daga sharrin ziina Ameen ya Allah BARKA DA JUMA A”

Ga wani:

ci gaban labarin soyayya me ban tausayi…

Yana daga kiran sai ya fara da gaisuwa bisa al ada, ta amsa Amma sai dai yanayin yadda ta amsa ya tabbatar masa da cewa akwai matsala. cikin fargabar yake tambaya, umma lafiya? ta dan yi shiru Bata bashi amsa ba, cikin tashin hankali khalifa ya Kara da cewa umma lafiya Dan Allah meke faruwa?

Karanta Wannan  Labarin soyayya mai ban dariya

Babu yadda ta iya haka ta danne zuciyata, muryarta na rawa take fadin Muna asibiti saudat na kwance a emergency Rai a hannun Allah. Innanillahi wa inna ilaihi rajiun ya fada tare da tashi a zabure, Yana fadin umma wani asibitine. Ta fada masa sunan asibtin sai akayi dace Basu da nisa sosai.
Fita yayi a gaggauce daga shi sai rigar barci ko wanke fuska bai yi ba. Yana tafiya kamar Wanda aka zare hankali daga jikin, ganin hakan ne yasa mahaifiyar khalifa ta tambayeshi ko lafiya Amma bai iya bata amsa ba haka ya fice ya tsayar da keke napep.

Ba shiri itama ta dauko nata mayafin domin bin bayansa sai dai Kash ya riga ya tafi. Amma tayi sa ar rike number keke napep din. cikin kankanin lokaci sai ga wani Mai Dan sahun ta hau tare da ce masa ya taimaka ya bi bayan duk inda napep dinsu khalifa yabi.

Badadewa khalifa ya Isa asibitin, I sarsa ke da wuya sai ya iske mahaifiyar sahibarsa, farin cikin zuciyarsa zaune tana ta Shar bar kuka kamar karamar yarinya. da kyar ya iya rike zuciyarsa ya Karasa inda yake ce mata mama Ina saudat Bata iya magana ba sai nuni kawai tayi masa, ya wai gawa sai ya emergency. cikin rauni da karayar zuciya ya ja kafarsa a hankali zuwa wata taga inda daga Nan ya hangi kaunar tasa cikin halinda Baki ba zai iya fadarsa ba.

khalifa Kara ya saki tare da yanke jiki a zube a wurin kamar matacce. Allah sarki soyayya gamon jini.

cigaban labarin soyayya me ban tausayi na khalifa da saudat Kashi na uku

innanillahi wainna ilaihi rajiun kawai kake ji ta ko Ina a yayinda nurses din dake kusa sukayi tururuwar zuwa inda khalifa yake kwance kamar gawa Kansa na zubar da jini saboda buguwa. ciki Suka shigar dashi a yayinda aka kwantar dashi tare da fara tsayar da jinin dake zuba a kanshi, sannan aka Saka masa oxygen don taimaka masa wajen numfashi.

A daidai lokacinne mahaifiyar sa ta karaso asibitin inda ta soma tambayar mahaifiyar saudat wacce take kuka shin Ina danta khalifa yake. Allah sarki baiwar Allah, cikin kuka take fadin khalifa ya Fadi Yana cikin emergency an kwantar dashi.
cikin karfin Hali da tawakkali take fadin innanillahi wainna ilaihi rajiun meyasame shi khalifa innanillahi wainna ilaihi rajiun.
samun wuri tayi ta zauna saboda yadda taji Jiri na Neman daukar ta. sun dan samu lkc me tsawo basu ce ta juna komai ba sai salati, ana cikin hakane mahaifiyar khalifa tayi karfin halin ta tambayi mahaifiyar saudat shin lafiya meya kawota asibiti, cikin karfin Hali itama da Bata labarin dukkan abunda ya faru da abunda yasa danta khalifa yazo asibitin. Ba shakka ta Fadi cikin takaici sannan ta cigaba da salati.
Bayan sallar ishai ne wasu nurses sukazo reception inda iyayen nasu suke tare da fadin kuje office ku biyun likita nason ganinku.

kwankwasa kofar office din sukayi, likitan ya amsa da yes come in. suna shigowa yayi musu nuni da kujera tare da fadin baba ku zauna mana ga waje.

zama sukayi cikin sanyi jiki tare da fargabar abunda likitan zai Fadi. bayan yagama duba wasu files sai ya dago da Kai tare da cewa wacece mahaifiyar mara lafiya ta farko. daga hannu mahaifiyar saudat tayi tare da cewar likita ni ce.
Ajiyar zuciya yayi tare da fadin jikin yarki alhamdulillah da sauki kuma ana samun nasara Amma gaskiya zuciyarta ta tabu sosai Dan Banda Allah yasa anyi gaggawar kawota zata iya rasa ranta. sallati tayi tare da fadin likita Kai taimaka mun ita kadai Allah ya mallakamin.

Karanta Wannan  Kalaman barkwanci a soyayya

Ya cigaba da nuna mata soyayya duk da wuta ta canja mata kamanni

Wadannan masoya labarin su yana da taba zuciya, Namijin sunanshi Micheal ita kuma macen sunanta Turia, sun fara soyayya tun a makaranta, koda yake shi Micheal ne ya nunamata soyayya lokacin amma ita tana kallonshine a matsayin abokin data shaku dashi kawai amma ba soyayyaba.

Sun kammala makaranta Micheal ya zama dan sanda ita kuma ta zama injiyar hakar ma’adanai, a lokacin soyayyarsu ta fara yin karfi, Turia ta amince dashi a matsayin saurayinta. Wata rana da dukansu bazasu taba mantawa da itaba gobara ta kama gida a lokacin Turia na ciki kuma ta kasa samun hanyar fita, Allah ya kaddara bata mutuba amma ta kone halittarta gaba daya ta canja.

Haka Micheal yazo ya rika zama da ita a asibiti lokacin bata san inda kanta yakeba, baya zuwa ko’ina, a karshema ya ajiye aikinshi saboda ya samu lokacin kula da ita dakyau. Jikinta ya kone kamanninta sun canja amma ko kadan irin son da yakemata be canja ba a zuciyarshi, kai asalima kamin ta farfado tasan inda kanta yake Micheal yaje ya samo zoben alkawarin aure ya yiwa kanshi alkawarin saiya aureta.

Bayan farfadowarta taga irin hidimar da yakeyi da ita kuma ta samu labarin cewa harya ajiye aikinshi, saita nuna damuwa tacemai ya kyaleta tunda dai ga irin yanda rayuwarta ta koma yaje ya samu wata sucigaba da rayuwa me dadi ta farinciki.

KADAN DAGA LABARIN SOYAYYA TA

Ni mutum ne ma’abocin San soyayya da Kuma kulawa wllh wannnan baiwar Allah tayimin komai a rayuwa lokacin da muka kasance ma’abota soyayya kullum burinta ta ganni cikin farin ciki ta kanyi kokari gusarmin da damuwar dake Kan fuskata Koda ban sanar Mata mai yake damuna ba wannan baiwar Allah din na kasa manta da ita a ciki tasawirar zuciyata

Mun dau dogon lokaci muna soyayya kamar bazamu rabu da juna ba ko da yaushe nakan tuna irin kalaman dake fitowa daga bakinta tabbas a wannan lokacin na gaskata soyayya cewa soyayya gaskiya ce, haka kawai wani lokacin sai ta kirani tace baby na kasa cin abinci Koda kuwa nasan cewa daga baya yunwar dake damunta dole tasa taci wannan abincin Amma sai naji dadi a zuciyata cewa ko Babu komai tana tunani a ciki zuciyarta tunda gashi har ta kirani a lokacin da take cikin Hali na yunwa

Na kasa mantawa da wannan baiwar Allah din duk lokacin da na tuna da ita sai na shiga wani Hali na rashin Dadi duk kuwa da cewa kafin ita nayi Yan Mata da yawa Amma yanayin da ita nakeji a kanta na dabanne

Kullum tunani waye ce wannan dayar da zata Soni ko muyi soyayya da ita ta mayemin waccan gurbin da na rasa

INA BUKATAR ADDU'ARKU ABOKAI TARE DA BANI SHAWARA SHEKARA DAYA DA WANI ABUN AMMA WLLH NA KASA MANTAWA DA ITA 

Kada kuga laifina ko ku zargeni akan hakan xaka iya rabu da mutumin kirki a rayuwarka guda daya kafin ka samu madadinsa xaka iya haduwa da gurbatattu goma, shawara kawai Dan allah.

Karanta Wannan  Sakonnin barka da safiya masu dadi

Ga Wani labarin.

Wata matace ta shiga dakin mijinta wanda yasha gyara tace mishi “baban Salim gaskiya ya kamata kayi kokari ka halarci wannan daurin auren na aminiyata. Sai yayi dariya yace ai zuwa daurin auren aminiyarki ya zama dole, yanzu me zaki kai mata gudummawa? Tace kudine dubu biyar, sai yace gaskiya biyar yayi kadan, ga goma ki kara.Ta karba ta mai godiya ta shirya ta tafi. Da aka gama biki kowa yayi haramar raka amarya gidanta, maman Salim ce babbar kawa ta kame a kusa da amarya. Abu kamar wasa taga an miki hanyar unguwarsu, sai tace ashema muna kusa, amaryar tace ai kusa sosaima. Bata ankara ba taga anyi parking a kofar gidansu, sai kuwa kowa ya fito, ta dubi direban tace malam ba nanne gidan ba, wannan gidanane. Nan fa musu ya hargitse, kwatsam sai ga miji (baban salim) da abokanshi, yana zuwa beyi wata wata ba sai ya rungume amaryarshi (watau amaryar da aka kawo) ya shige da ita gidan har cikin dakinshi. wannan goron sallah ne daga naku

DAN ALHAJI

Allah yamai maita mana

LABARIN KWADAYYAYIYAR AMARYA
ANZO ACI BANZA

Assalamualaikum Barkanku da yamma Dan Allah inaso ku taimaka min da shawara, nayi Aure wata na 5 kenan amma wlh auren yafita raina na rasa yanda zanyi gashi dai inason mijina

Akwai wata maqociya ne tunda suka Siya gida a anguwar mu dai Ina shiga gidan Ina tayata aikace-aikace Wani lokaci ma idan mijinta yayi tafiya Ina zuwa gidan Ina tayata kwana mun Kai tsawon 3years da ita har ta haihu Nike kulawa da baby dinta, Yaranta 3 Ina zuwa in kaisu makaranta wata rana in dawo dasu, to wlh irin gidan sunada rufin asirin su Dan wlh da kyar kiga anyi girki gidan nan babu nama, haka kawai zakiga Muna aikin kaji (chickens) wata rana muyi pepper soup din cat fish ko na kayan ciki da sauran su, matar gidan kuwa da nake tayata aiki wlh idan ki ka ga irin dressing din da takeyi wlh ke kanki kinsan kudin ya zauna gold kala kala tana dasu da sauran su, kawai sai naji soyayyar mijinta ya shiga raina wlh, ashe Shima Yana So na

Ranar daya fara bayyana min soyayya na Amince dashi, Koda yace mata zai aureni Bata damu ba wlh tace Allah ya Bamu zaman lafiya kawai dai tace in daina zuwa mata aiki sbd na wuce yar aiki yanxu matar gida nake, da bikina ta bani gudumawa na 50K akayi biki aka wuce wajen, wlh in Baku labari ashe duk dadin da naga ana ci a gidannan uwar gida na ke Siya da kudinta, shi mijin mu bayida komai wlh sai rufin asiri, anci gaba da cin dadi a gidan amma banda ni saidai ita da Yaranta da da mijinta, Shikam Bata canza mishi ba, har gidan ma nata ne wlh, in gaya Muku yau 5days kenan ni shinkafa da mai da yaji nakeci shine Wanda mijinmu ya kawo min ita Kuma kudinta takeci, ko jiya wlh papper chicken sukaci a tsakar gida Amma basu bani ba, naje na dauki yarinyar ta inata mata wasa ko zata bani amma wlh duk da haka ta hanani, Dan Allah ku bani shawara ya zanyi Ina cikin damuwa wlh

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *