Tuesday, May 27
Shadow

Likitocin Abuja za su tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata

Kungiyar ƙananan likitoci a Najeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Talata, bayan korar ma’aikatan lafiya 127 da hukumar kula da ma’aikatan birnin na FCT ta yi.

An yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa da kungiyar likitocin ta gudanar a asibitin Asokoro ranar Litinin, kamar yadda kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito.

Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr. George Ebong, ya bayyana korar a matsayin maras tushe da kuma “rashin imani”, yana mai buƙatar gaggauta dawo da ma’aikatan bakin aiki tare da biyansu albashin watan Afrilu.

Dr. Ebong ya kuma buƙaci shugaban hukumar kula da ma’aikatan Abuja, Emeka Ezeh, da ya yi murabus daga mukaminsa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda wani Kirista ya shiga Masallaci ya samu Liman ya mai karyar shi sabon musulunta ne, yana son a koya masa yadda ake sallah, Ko da Limamin yayi sujada sai ya zaro wuka ya caka mai fiye da sau 40

Ya yi gargaɗin cewa idan Ministan Abuja Nyesom Wike bai ɗauki mataki cikin kwanaki uku ba za su shiga yajin aiki na sai baba-ta-gani tare da rufe duk asibitocin Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *