Thursday, January 8
Shadow

Ma’aikatar Noma tace ma’aikatanta su dauki azumin kwana 3 dan yin Addu’a a samu wadataccen Abinci a Najeriya

Ma’aikatar Noma ta Najeriya ta yi kiran da a dauki Azumi a tsakanin ma’aikatan hukumar dan neman Allah ya wadata kasa da Abinci.

Sanarwar hakan na kunshene a cikin sanarwa wadda wakilin ma’aikatar, Adedayo Modupe ya fitar inda yace ana bukatar addu’ar domin taimakawa kokarin Gwamnati na wadata kasa da abinci.

Yace ana tsammanin duka ma’aikatan hukumar zasu fara wannan Azumi dan neman taimakon Allah.

Sanarwar ta bukaci kowane ma’aikacin hukumar ya dauki azumi ranar Litinin ya je dashi wajan aiki.

Karanta Wannan  Kaso 35 cikin 100 na ruwan Najeriya ne kadai sojojin ruwa suke iya tsarewa, sauran Kamfanoni masu zaman kansu aka dauka aka baiwa kwangilar aikin>>Inji Sowore

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *