Friday, January 24
Shadow

Maganin goge tabo a fuska

Tabon fuska matsalace dake damun mata da yawa, kuma akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan goge shi.

Ga wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani dasu wajan goge tabon fuska kamar haka:

Amfani da Aloe Vera: Ana amfani da mai ko ruwan Aloe Vera wajan goge tabon fuska kuma yana aiki sosai, ana iya sayen man Aloe Vera a shagon saida mai wanda ba’a hadashi da komai ba, a duba roba ko kwalin man a tabbatar ba’a hadashi da giya ba ko wasu abubuwa na daban ba, kamin a siya, mafi kyawun hanyar samun mai ko ruwa Aloe Vera shine a hadashi a gida.

Karanta Wannan  Maganin kurajen fuska

Ana samun ganyen Aloe Vera a kankare koren ganyen dake jikinshi a matso ruwan a rika shafawa a fuska dan maganin tabon fuska, mun yi cikakken bayani kan yanda ake amfani da Aloe Vera wajan gyaran fuska

Hakanan ana amfani da Zuma wajan cire tabo a fuska, yanda ake yi shine, ana samun zuma me kyau a shafata a fuska, a bari ta yi mintuna 10 zuwa 15 sannan a wanke. Mun yi cikakken bayani kan yanda ake amfani da zuma wajan gyaran fuska.

Hakanan ana amfani da Kurkur wajan cire tabon fuska, yanda ake yi shine ana hada Kurkur da Yoghurt ko Zuma a kwaba a shafa a fuska. Mun yi cikakken bayani yanda ake amfani da Kurkur wajan gyaran fuska.

Karanta Wannan  Hadin man gyaran fata

Ana kuma amfani da Farin ruwan Kwai wajan kawar da tabon fuska, yanda ake yi shine, Ana fasa kwai a cire gwaiduwar a bar farin ruwan a hada da zuma ko kurkur a juya sosai a rika shafawa a fuska, mun yi bayani kan yanda ake amfani da farin ruwan kwai wajan gyaran fuska.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *