Akwai maginin likita na kaikayin Dubura sannan akwai dabarun da mutum zai yi a gida dan magance wannan matsala.
A wannan rubutu, zamu bayyana dabarun da za’a iya amfani dasu ne a gida dan magance wannan matsala.
Hanya ta farko ta magance kaikayin dubura shine a tabbatar ana wanke jiki da kyau idan an kammala yin kashi.
Kada a sa sabulu me kanshi ko a shafa mai ko turare a wajan, kada a goge wajan da tsumma me kaushi, a wanke da ruwa kadai ya wadatar.
Idan an ji kai kayi, a daure kada a sosa, sosa kaikayin dubura zai iya maka dadi ko ka dan ji saukin abin na dan lokaci amma abinda yafi shine kada a sosa. Idan abin yayi yawa, ana iya yin wana da ruwan dumi dan samun sauki.
A gujewa saka kaya masu matse jiki da zasu iya shiga tsakanin mazaunan mutum su makale, hakan zai karawa kaikayin dubura tsanani.
A rage ko a daina cin wadannan abincin har sai an samu sauki, Tumatir, Abinci mai yaji, shan lemukan zaki, shan giya da cin Abincin da aka sawa magi sosai.
A yawaita cin Wake, Aya, Masara, dawa, gero, da sauransu wanda ke da dussa a jikinsu har sai an samu sauki.
Ana kuma iya shafa farar hodarnan ta Gwangwani ko kuma aje a nemi nonmedicated hoda a ruka shafawa.
Ana iya samun tsumma me kyau wanda bashi da kaushi, ko kuma a samu auduga a rika tsomata a ruwan sanyi ana sawa a duburar.