Friday, December 6
Shadow

Menene maganin wasa da gaba

Wasu Mata da maza, Musamman wadanda basu da aure sukan yi wasa da gabansu dan su gamsar da kansu a duk sanda sha’awarsu ta motsa.

Wannan abu da ake yi, yakan iya zama yau da gobe watau har ya zamana ya zamarwa mutum dabi’a mw wahalar dainawa.

A daidai lokacin da abin ya zamarwa mutum dabi’a, kuma ya kara hankali, sai ya ga cewa ya kamata ya daina,anan ne sai a fara neman magani.

To maganar gaskiya babu wani magani na likita ko na gargajiya da ake sha dan ya hanaka ko ya hanaki yin wasa da gabanka ko gabanki.

Dalili kuwa, dabi’a ne ba cuta ba.

Karanta Wannan  Amfanin tsotsar farjin mace

Ita kuwa dabi’a, mutum ne da kansa yake hana kansa yi, saidai akan iya bayar da shawarwari.

Misali idan mutum na son ya daina wasa da gabansa, ya kamata ya kiyaye wadannan abubuwan:

Ya daina kallon Fina-finan batsa.

Ya daina hirar batsa.

Ya daina yawan zama babu abinda yake yi.

Dan rage karfin sha’awa mutum ya rika yin azumi.

Babban maganin abin shine mutum yayi Aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *