Sunday, January 5
Shadow

Maganin yawan kukan jariri

Ba matsala bane kukan jariri, masana kiwoj lafiyar yara sun bayyana cewa, jarirai zasu iya yin kuka na tsawon awanni 2 zuwa 3 kullun daga ranar da aka haifesu har zuwa tsawon sati 6.

Hakanan masanan sun ce a watanni 3 na farko da aka haifi jariri yafi yin kuka sosai fiye da kowane lokaci.

Yawanci kukan jarirai yana raguwa ne a yayin da suka kai watanni 3 zuwa 4 da haihuwa a Duniya.

Abubuwan da zaki yi idan jaririnki yana yawan kuka sun hada da:

Ki tabbatar ba zazzabi ne ke damunsa ba.

Ki tabbatar Fanfas dinsa ba kashi ko fitsari a ciki.

Kina iya daukarsa ki dan yi tafiya dashi.

Kina iya yi mai magana, kamar yi shiru, yi shiru, ko ki dan mai wasa haka.

Kina iya mai wanka da ruwan dumi.

Kina iya rika shafa masa baya ko daddaba masa baya.

Kina iya kifashi akan cinyoyinki ki rika shafa masa baya.

Kina iya masa karatun Qur’ani.

Jarirai dake kasa da watanni 2 sun fi so su kwanta a gadon bayansu.

Kina iya kiran danginki su taimaka miki da rainon yaron ko kuma idan yaki yin shiru, ki kwantar dashi a gadon bayansa ki dan koma gefe ki ci gaba da ayyukanki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *