Tuesday, October 13
Shadow

Mahaifiya data kai danta yayi Karatun Qur’ani, kammala amma bata raye

Allah Sarki, Labari me taba zuciya.

Wannan yaron mahaifiyarsa ta kaisa makarantar Haddar Qur’ani, ta mikashi hannun malamin tace duk abinda za’a masa a masa na ladaftarwa ita dai bayan shekara daya tana son ta ga ya zama mahaddacin Alqur’ani.

Malaminsa dake bayar da labarin Yace aka fara karatu.

Sai ta Kwanta jinya.

Malamin yace ya dauki dalibin me suna Isma’il Muhammad suka je duba mahaifiyar a Asibiti

Yace da suka je dubata, tana kwance a gadon Asibiti, ta rike hannun danta, tace abinda nake so da kai shine ka zama mahaddacin Qur’ani.

Yace bayan sun koma makaranta, ta sake kiran malamin tace wasiyyarta shine tana soj danta ya zama mahaddacin Qur’ani.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Wasu Tshàgyèràn Dhàjì da aka kama sun bayyana jami'an Gwamnatin dake basu Màqàmài

Amma yau gashi yaron ya haddace Qur’ani amma bata raye

https://www.tiktok.com/@rabealiyu07/video/7685795714701528338?_r=1&_t=ZN-99nuYTYh21L

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *