
Rahotanni sun bayyana cewa Kwamitin majalisar Dattijai dake aiki kan gyaran kundin tsarin Mulki ya amince da samar da savuwar Jiha a yankin Inyamurai.
Idan aka kirkiro wannan jiha, yankin na Inyamurai zai zamo daidai da sauran yankunan kasarnan watau suma zasu zamana suna da jihohi 6 kenan.
A halin yanzu dai yankin na Inyamurai sune kadai yankin dake da Jihohi 5 kadai watau Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo