Wednesday, September 2
Shadow

Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya nemi kotu ta bashi damar zuwa Asibiti dan a duba idansa da hakoransa

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya nemi kotu ta bashi dama ya je a duba lafiyar idansa da ta hakoransa.

El-Rufai ya nemi hakan ne a gaban babbar kotun jihar Kaduna inda ICPC ta sake gurfanar dashi dan bayyana sabbin tuhume-tuhumen da take masa.

Kotun dai ta amince da wannan bukatar ta malam Nasiru Ahmad El-Rufai inda tace amma Asibitin da za’a dubashi kada ya wuce Abuja.

Sannan a tabbatar jami’an ICPC zasu bishi.

Karanta Wannan  Dole Tinubu ya dauki mataimaki Kirista ko kuma ya fadi zabe a 2027>>Inji Wata Kungiyar Kirista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *