
Rahotanni daga Makurdi Jihar Benue na cewa masu garkuwa da mutane sun sace dalibai biyu daga jami’ar Joseph Sarwuan Tarka University dake jihar.
An yi garkuwa da dalibanne a daren ranar Talata a gaban makarantarsu.
A hirar da aka yi da daya daga cikin daliban me suna Ashar Lubem ya bayyana cewa dalibai 4 ne aka yi garkuwa dasu kuma lamarin ya jefa daliban makarantar cikin rudani.
Kakakin ‘yansandan jihar, Sewuese Anene ta tabbatar da faruwar lamarin saidai tace dalibai 2 ne kadai aka yi garkuwa dasu kamar yanda suka samu bayanai.
tace kuma suna kan binciken lamarin.