
Wata kungiyar mata daga yankin Kudu maso kudu a jihar Bayelsa ta fito zanga-zanga akan rikicin sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio.
Kungiyar matan tace kada Sanata Natasha Akpoti ta zubarwa da Sanata Godswill Akpabio mutuncinsa da ya dade yana karewa.
Sun yi Allah wadai da halinta inda suka ce ba irin halin matan Najeriya bane, kamar yanda daya daga cikin matan me suna Hon. Ebiere Akpobasa ta bayyana.