Wata mata me shekaru 33 a kasar Afrika ta kudu ta dirkawa mijinta harsashi ya mutu har lahira bayan data kamashi yana lalata da wata.
Tuni dai hukumomi suka kama matar bisa zargin kisan kai.
Suna zaune gida dayane dai da matar da mijin yayi lalata da ita.
Kuma da matar tasa ta fuskanceshi da maganar, sai yayi yunkurin tserewa, saidai ta yi amfani da bindigarsa ta harbeshi ya mutu.
Kakakin ‘yansanda na yankin Limpopo, Col Malesela Ledwaba ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace auna bincike.