Monday, June 2
Shadow

Matata tace Na burgeta kuma zan yi kyau da Fafaroma shiyasa na watsawa Duniya ta gani>>Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yayi karin bayanin dalilin da yasa ya wallafa hotonsa da kayan Fafaroma

Bayan da cece-kuce yayi yawa akan hoton da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya wallafa yana sanye da kayn Fafaroma, ya fito yayi karin bayani.

Shugaba Trump yace Kamin ya dora hoton a shafinsa na Sada zumunta sai daya nunawa matarsa kuma ta amince dashi cewa yayi kya.

Yace dan haka yayi amannar kasancewar matarsa ‘yar Darikar Katolika, to yasa sauran ma ‘yan darikar zasu so hoton.

A baya dai da aka Tambayeshi wa yafi cancanta ya zama Fafaroma, sai yace shine.

Karanta Wannan  An kama magidanci da Abokinsa da sukawa Agolarsa fyàdè, suka dirka mata ciki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *